• Dalilan Da Suka Sa Farashin Albasa Yayi Tashin Gwauron Zabo
    Dec 12 2024

    Send us a text

    Albasa na taka muhimmiyar rawa wurin kara wa abinci armashi ko dai ta hanyar kara dandano da kamshin girki, kai a wasu lokutan ma alumma kanyi amfani da albasa saboda likitoci sun bayyana cewar yana kara lafiya ga jikin dan adam.

    Sai dai a kwanan nan, an wayi gari albasar tayi karanci a kasuwanni wanda hakan yasa aka samu karuwar farashin ta a kasuwanni da ma manyan dilolin ta.

    Shirin Najeriya A Yau na wannan rana ya zanta da masu ruwa da tsaki kan batun Albasa, dalilan tashin farashin ta da kuma hanyoyin samun maslaha.

    Show More Show Less
    25 mins
  • Yadda Matsalar Cin Zarafin Mata Ta Zama Karfen Kafa A Najeriya
    Dec 10 2024

    Send us a text

    Cin zarafin mata a Najeriya matsala ce da ke ci gaba da ci wa masu ruwa da tsaki a Najeriya kwarya.

    Hanyoyin cin zarafin na mata dai suna da yawa; kama daga lakada musu duka zuwa yi musu fyade da wasu abubuwan da dama.

    Ko wanne irin hali mata suke shiga sakamakon cin zarafi a gidajen aurensu?
    Shirin Najeriya a Yau zai yi magana da matan da aka ci zarafinsu da ma mazan da suka ci zarafin matansu don gano bakin zaren.

    Show More Show Less
    26 mins
  • Kuncin Da Marasa Lafiya Suke Ciki Sakamakon Tsadar Magani
    Dec 9 2024

    Send us a text

    Farshin maganin asibiti yana ci gaba da tashin gwauron zabo a Najeriya, inda yake jefa marasa lafiya da ’yan uwa da abokan arziki cikin halin tsaka mai wuya.

    Da yawa daga cikin marasa lafiya dai sukan koma amfani da abin da ya fi musu sauki – ko dai sayen maganin a hannun masu tallansa a kafada, ko amfani da maganin gargajiya, ko kuma, a wasu lokutan, hakura da maganin.

    Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan halin da marasa lafiya sukan shia sakamakon tashin gwauron zabo da maganin asibiti ya yi.

    Show More Show Less
    23 mins
  • Abin Da Ya Sa Ake Hana ’Yan Najeriya Fadin Albarkacin Bakinsu
    Dec 6 2024

    Send us a text

    Sashe na 4 na kundin tsarin mulkin kasa na dauke da tanadetanade musamman da suka shafi ‘yancin dan adam a dokar Najeriya.

    Cikin tanade-tanaden akwai ’yancin da doka ta bai wa kowane dan najeriya na rayuwa, da shiga taro, da fadin albarkacin baki.

    Shirin Najeriya A Yau zai yi duba a kan tanade-tanaden doka a kan ’yancin fadin albarkacin baki.

    Show More Show Less
    24 mins
  • 'Karambanin' Malaman Musulunci A Kudurorin Haraji Na Tinubu
    Dec 5 2024

    Send us a text

    Kudurorin Dokar Haraji da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike wa Majalisar Dokoki ta Kasa suna ci gaba da tayar da kura a Najeriya.

    Muhawara a kan batun ta dauki sabon salo ne bayan da wasu malaman addinin Musulunci daga Arewacin Najeriya suka ki amincewa da wasu tanade-tanaden kudurorin dokar.

    Shin har da kaza ne a cin danko? Karambani ne ya sa malamai tsoma baki a muhawarar ko neman maslaha ga al’umma?
    A kan wadannan batutuwa shirin Najeriya A Yau zai yi nazari.

    Show More Show Less
    27 mins
  • Dalilin Ƙulla Yarjejeniyar Gwamnatin Kaduna Da ’Yan Ta’adda
    Dec 3 2024

    Send us a text

    Yankin karamar hukumar Birnin Gwari dake jihar Kaduna na daya daga cikin alummomin da suka fi fuskantar matsalar tsaro musamman a arewacin Najeriya.

    A kwanan nan rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin jihar ta shiga yarjejeniya tsakanin yan bindigan da kuma gwamnatin jihar.

    Shirin Najeriya A Yau yayi Nazari ne kan wannan yarjejeniya da kuma abun da hakan ke nufi ga jihar da ma alummar yankin.

    Show More Show Less
    28 mins
  • Dalilan Yawaitar Gobara A Lokacin Hunturu
    Dec 2 2024

    Send us a text

    Lokacin hunturu lokaci ne da sau da yawa akan fuskanci barazanar tashin gobara a sassa da dama na Najeriya.

    A wasu lokutan kuma, abubuwan da mutane suke yi kan taka muhimmiyar rawa wajen tayar da gobara a gidaje, da kasuwanni da ma sauran wuraren zamantakewar jama’a.

    Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan da suka sa aka fi samun gobara a irin wannan lokaci da kuma hanyoyin da za a bi wajen hana aukuwarta.

    Show More Show Less
    26 mins
  • Kalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyan 'Ya'yan Su
    Nov 29 2024

    Send us a text

    Duk wanda ya shekara arbain zuwa sama ya san irin tarbiyyan da ya samo daga wurin iyayen sa a da baya can, irin mu’amalan dake tsakanin sa da iyaye har ma da shakuwan dake tsakanin ‘ya’ya da iyaye.

    A yanzu kuwa abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincabe sukayi wa iyaye yawa.

    Daya daga cikin manyan sauyin da aka samu sun hada da aikin gwamnati ko aikin wata da iyaye mata suke yi a wannan zamani wanda hakan a wasu lokuta ke barazana ga irin kulawan da ‘ya’ya suke samu.

    Shirin Najeriya A Yau zai yi Nazari ne kan irin kalubalen da iyaye ke fuskanta a wannan zamani wajen tarbiyyan ‘ya’yan su.

    Show More Show Less
    27 mins